Ranar da na'urar MTN ta samu tangarda mutane da dama sun kwasi gara'basar tsarin shiga yana (Data) har 128gb amman muna ganin kamar murna zata koma ciki bayan da kamfanin ya d'arma d'amarar maido dukiyar su da wasu masu amfani da layukkan MTN sunka kwasa. Wata majiya ta bada cewar matsalar ta ja ma kamfanin sadarwar mallakin kasar Afrika-ta-kudu asarar kudi da kimaninsu zai kai Naira Miliyan dari bakwai (N700,000,000) cikin sa'o'in biyu (2 hours) da matsalar ta abku. Ance kamfanin ya tuntubi hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta duba kundin dokar satar yanar gizo (Cybercrime) wanda zai yi sanadiyar cire Naira dubu hamsin(N50,000) kan 128GB daga wadanda layukkansu ke hade da akwatunan bankunansu. 
Wata majiya ta ce wasu layukkan MTN da sunka kwasi gara'basar ta amfani da tarkacen lambobi kamar haka *131*7*5*1*1# an kullesu tsawo sa'o'i  24 inda kamfanin ya cigaba da kwashe tsarin shiga yanar dinsu da mutane sunka samu sanadiyar tangardar.