Dukkanin mu mun san cewa matsalar riƙon wuta na ɗayan daga manyan matsalolin dake tattare da sanannar manhajar nan Android, yawancin ma wayoyinsu na zamani. Saboda haka dan a shawo kan matsalar, makeran wayoyin irin su Tecno, Itel, Infinix, Samsung, Sony Xperia d.s.s ke ta jibge sabbin wayoyi a kasuwa dake da yawancin rikon karfin wuta ko kuma dai ana cigaba da ƙerasu da yawa dan shawo kan matsalar ta shan wuta ga wayoyin.

Amman kamin wannan cigaban, akwai wasu dubarori na azancin da muke yi, wanda kafar BagoTech zata bayyano muku dan ku ma ku tsawaita karfin wutar wayoyinku na zamani. Amman ga Baturori masu ƙananan (Milliampere hour); 950mAhs, 1000mAhs, 1500mAhs, 1700mAhs da makamanta, za'a iya kuma amfani da waɗannan dubarorin ga Baturori masu alamar  2500mAhs, 3000mAhs kai har ma fiye in kunka bi waɗanga matakan da munka bayyana a ƙasa:

Yanar Gizo:
Ku kashe dukkan ayyukkan dake buƙatar shiga yanar gizo da makamanta: Shiga ta wifi, bluetooth da Data, a kashe su matat. Sune jigon shan wutar Wayoyin Android da sauran su. Shawara anan ita ce ku bar barinsu kunne.

Ku kashe tsarin yanar gizo na bangon waya in ba'a bukata tai: A kashe shi, in ba'a son aiki dashi, yana shan wuta da kuma cinye Tsari shiga yana (Data plan) makuƙa.

Ayukka:
Ku cire dukkan ayukkokin dake kan waya in sun yi yawa: Danne alamar Minimise a ciccire dukkan manhajoji da wasannin da aka gama aiki dasu. Suna jinkirtarda wayoyinku da kuma taimakawa wajen tsutsar wutar Baturorinku, dan haka cicciresu shine makawa.

Hasken Waya:
Rage hasken waya: yawan haske zai iya bada kamar da ake so ga wayar zamani ko kuma haskaka bangon wayar, amman ba haka abun yake ba. Hasken waya na daga abubuwan dake shan wutar Wayoyin Android, Symbian, Java d.s.s

Hoton bango(Wallpaper):
Hauda hoton ainahi wato marar motsi: Sake hoton nan mai je ka ka dawo, ruwa-ruwa, zane-zane, gewaye-gewaye, jere-jere da makamanta. Suna shan wutar wayoyinku fiye da yanda baku tsammani saboda motsin nan da suke.

Manhajoji da wasanni:
Cire manhajoji da kayan wasannin da basu da amfani ko waɗanda baku aiki dasu. Suna ɗauke nauyin ƙwaƙwalwar wayoyinku wanda ke taimakawa wajen shan wuta. Ku cicciresu dan ku samu shakat!

Kashe sadarwa:
Kashe dukkan ayyukkan shiga yanar gizo-gizo, irinsu Bluetooth, Wifi, Gps, Data "3g da sauranau sanda ba'a bukatarsu. Shiga yanar gizo na ɗayan daga abubuwan dake sa shan wutar wayoyinku na tafi da gidanka, amman bamu da makawa wadda ta fi kunna sadarwar "2g" tunda bamu iya yi ba tare da ita ba. Kunna sadarwar "3g'' in za'a ƴan kallace-kallace ko in ana buƙatar shiga mai sauri.

 Kiɗe-kiɗe(Music playing):
A yi ƙoƙari a ga an rage yawan kaɗe-kaɗe, duk da cewa bai kai yanar gizo shan wuta ba.

Da karshe, dan kyautata karfin wutar baturi ku yi ƙoƙari ku ga kun cizge wayarku ta Android, wato ku yi mata (root), a kuma hauda manhajoji dake tabbatarda da kayyade ayukkan wutar Andriod. Ga manhajojin da zamu iya wajabta muku ku girka ga wayoyin naku dan kayyade shan wutar wayar Andriod ɗinku. An jerasu dangane da amfaninsu da tsarukkansu: DU Battery Saver, Battery Doctor, Juice defender, Easy Battery Saver, Battery Defender, Avast Battery Saver, Battery Optimizer & Cleaner by McAfee, 3x battery saver – iBattery, Battery Aid – Saver & Manager da CM Battery.