Kusan dukkan manhajojin (Applications) da muke girkewa a wayoyinmu na zamani, Android, na lalubar tsarin shiga yana (Data plan) da yawa dan tabbatarda kyakkyawan ayikkansu. Dukkan Manhajojin da ake daukowa na sabuntuwa duk sanda wayar ke kunne kuma in shi ma tsarin na shiga yana na kunne.
In dai tsarin shiga yana na kunne, to dukkan Manhajoji da basu da sabunta na sabuntuwa dole, ko da ba yawancin tsarin na shiga yana, daga nan sai cinye tsarin shiga yana da kyabtawa da bismillah, sai dai in mutum ya kayyade iyaka(limit). Baƙin cikin abun kuma shine in kwana ya dauke mutum ko ya shagaltu da aiki, kuma wayar na kunne. Ba abunda zai ragu kenan.

Tsarin yana na "Background data" zai dakatu dan rage cin tsarin shiga yana da kuma yawan shan wuta ga Wayoyin Android. Matsalar da zaku fuskanta ita ce ba zaku rinka samun sanarwar sabuntar Manhajojin da aka sabunta ba ko dauko sabbin Manhajoji daga Google playstore ba a ƙayyade(Automatically) dole sai in an sake kunna ta. Ku kunna ta in akwai wadatattar Data.
Yanzu, sai mu komo ga yanda zamu kashe tsarin yana na bangon waya (Background data).
Wani abun kallo shine yawancin mutane sun gwammacema amfani da Manhajojin Android na musamman dan dakatarda wannan tsarin da cin Data. Amman kuma, gaskiya magana ita ce waɗannan Manhajojin na musamman bata lokacine da kuma tattare Ƙwaƙwalwar Wayoyinku. Ita kanta zabayar, Android nada tsarin tattare da ita. Zaku iya dakata tsarin yanar na bango ga dukkan Manhajojin ko ga zaɓaɓɓun manhajoji ta bin waɗanga hanyoyin da aka banyana kasa.
Dakata tsarin bango "Background data" ga kowane Manhaja (All Applications):
A ire-iren wayoyin Android 4+, ku taba Settings>> Data usage>> Menu. Zaku ga zabukka da dama a nan, kamar yanda yake bayyane ga hoton (screenshot) dake kasa. Yanzu sai ku cire zabin "Restrict background data". In kun gama da wannan, tsarin yanar na bango zai dakatu kuma za'a gwada muku kamar yanda ya bayyana ga hoton (screenshot) kasa. Bi wagga hanyar ga ire-iren Android version 2s Settings> Accounts & Sync a kuma cire zabin na "Background data".

Dakata tsarin cin yanar na bango ga zaɓaɓɓar Manhaja ( Selected Application):
Dan kashe tsarin yana na bango ga zababbar manhaja da aka ga tana yawan cin Data, bi wagga hanyar. Shiga matattaran Settings>> Menu a taba zabin Data usage. Zaku ga manhajojin jere dangane da wanda ya fi jan tsarin shiga yana (Data), kamar yanda yake bayyane ga hoton (screenshot) dake kasa. Zaku ga karin zabukka biyu in kun taba manhajar kamar  "Foreground" da "Background". A kasan karshe, zaku ga zabi na dakatarda tsarin yana na bango (Restrict background data). Cire zabin dan dakatarda tsarin yanar na bango. In kuna son kashe tsarin yana na bango ga sauran manhajojin to sai ku maimaita yanda kunka yi a baya. Shikenan